Wasu kungiyoyi sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiyar Bola Tinubu zuwa Paris

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al’ummar Igbo da wasu kungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiya zuwa Paris da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro.

A ranar Laraba 24 ga watan Janairu ne shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta kashin kai.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Najeriya cikin makon farko na watan Fabarairu.

Sai dai kungiyoyin a hirarsu da manema labarai sun koka cewa babu gaskiya cikin sanarwar tafiyar la’akari da yadda aka kira tafiyar ta “kashin kai”.

Matakin kungiyoyin na zuwa ne bayan da shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki Tinubu inda ya bayyana shakku game da makasudin tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake fuskantar karuwar matsalar yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara. Sai dai Fadar shugaban kasar ta ce duk da cewa Tinubu ba ya kasar, yana aiki tukuru domin kawo saukin matsalolin kuma yana bai wa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke bukata domin samun nasara kan masu aikata miyagun laifuka da nufin fitar da Najeriya daga halin rashin tsaron da take ciki.

Comments (0)
Add Comment