Wani Mutum Yayi Ƙarar Matarsa Saboda Tana Haifa Masa Ƴaƴa Munana

Wani mutum Mai suna Sin Jian feng ya yi karar matarsa saboda Haifa masa munanan ’ya’ya,
“Na auri matata saboda soyayya, amma lokacin da ta fara haihuwar ’ya ta farko sai muka fara samun matsala da ita,” kamar yadda ya bayyana wa mane ma labarai. “’Yarmu ta yi matukar muni, har ta kai ga tana ba ni tsoro”.

Da farko Jian ya zargi matarsa da lalata a waje, saboda yana da tabbacin cewa babu yadda za a yi ya zama uba ga mummunan ɗa, Sai dai da aka gudanar da gwajin kwayoyin halitta sai aka tabbatar masa cewa nasa ne.

Da aka wanke matarsa daga zargi, daga baya sai ta fito ta bayyana masa gaskiya cewa, an yi mata kwaskwarimar gyaran siffa ne, inda ta kashe Dala dubu 100 wajen aikin a kasar Koriya ta Kudu kafin haduwarsu.

Feng ya yi karar matarsa kan yaudararsa da ta yi ta hanyar kin bayyana masa gaskiyar yadda aka gyara mata siffa ta zama kyakkyawa, har ta kai ga damfararsa ya dauka ita kyakkyawa ce.

Alkali ya amince da hujjar Feng, don haka ya bayar da umarnin matar ta biya shi Dala dubu 120.

Comments (0)
Add Comment