Wani abin fashewa ya fashe a wata gona a kusa da kasuwar Mammy da ke Legas

Rundunar sojin Najeriya tace  wani abin fashewa ya fashe a wata gona a kusa da kasuwar Mammy da ke cikin gundumar Ikeja a Legas jiya Litinin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a Abuja.

Mista Nwachukwu ya ce ana kyautata zaton fashewar ta faru ne sakamakon kona shara da wasu tarkace bayan da wani manomi ya girbe amfanin gonar sa. A cewar sa, ba a samu asarar rai ba a lamarin.

Comments (0)
Add Comment