Wadanda ke rike da akalar gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Solomon Dalung

Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya a zamanin shugaba Buhari, Solomon Dalung, ya ce mutanen da ke juya gwamnati ta bayan fage waɗanda ake kira ‘cabal’ na mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sun fi na zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari haɗari.

Dalung ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce a zamanin mulkin Buhari, wasu mutane sun riƙa juya akalar gwamnatin.

Sai dai ya ce waɗanda suka juya mulkin Buhari ba su da ilimi da wayewa sosai, amma waɗanda suke juya gwamnatin Tinubu sun fi ilimi da sanin mulki kuma sun fi tarin buri.

Dalung ya ce, “lallai akwai masu juya gwamnati ta bayan fage a zamanin Buhari. Amma mutanen wancan lokacin ba su da ƙwarewa sosai a kan mulki da siyasa, don haka tasirin ya taƙaitu. Amma waɗanda suke mulkin Tinubu, sun fi wayewa kuma sun fi ilimi da sanin ƙarfin mulki. Wannan ya sa gwamnatin za ta sha wahala sama da na zamanin Buhari.”

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment