Hukumar zaɓen Najeriya, Inec ta bayyana cewa waɗanda suka tura koke da takardun sanya hannu kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye ba su sanya da ake buƙata ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da hukumar ta fitar a yau Talata, wanda ya samu sa hannun mai magana da yawun hukumar, Sam Olumekan.
Sanarwar ta ce “abin da hukumar ta lura da shi bayan kawo ƙorafin shi ne waɗanda suka jagoranci kawo ƙorafin ba su bayar da adireshi da lambobin waya da kuma adireshin tura saƙon email da za a iya tuntuɓar su ba.
“Adireshin kawai da aka rubutu a jikin takardar shi ne ‘Okene, jihar Kogi’, wanda wannan bai isa a iya tuntuɓar masu ƙorafin ba,” in ji sanarwar.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa “lambar wayar jagoran masu turo da koken ne kawai a saka a wasiƙar, maimakon lambobin wayoyin dukkanin wakilan masu ƙorafin.”
A cikin sanarwar, INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin suka cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.
Sanata Natasha Akpoti na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ta da shugaban majalisar dattijan Najeriya, Godswill Akpabio, bayan zargin da ta yi masa na yunƙurin cin zarafi na lalata.
Sai dai majalisar dattijan ta zargi Natasha da karya dokokin majalisa ta hanyar ƙin komawa sabuwar kujerar da aka sauya mata, da kuma yin hargowa a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisar na tsawon wata shida.
Yanzu haka dai hukumar zaɓen Najeriya ta tabbatar da cewa an kai mata ƙorafin neman yi wa ƴar majalisar kiranye, inda aka tura mata takardu ɗauke da sa hannun rabin masu kaɗa ƙuri’a 474,554 na rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓar ƴar majalisar a ƙananan hukumomin Adavi da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene.