Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF na ci gaba da hada hannu da wasu hukumomi domin ceto rayukan dubban yara marasa gata, da kuma kyautata rayuwar su.
Daya daga cikin yunkurin na asusun UNICEF shi ne samar da wasu cibiyoyi na horas da almajirai da ‘yan mata masu tasowa wadanda ba su samu damar zuwa makarantun boko ba, yadda zasu koyi ilimin na’ura mai kwakwalwa da na yanar gizo.
Humukomomi sun jima suna nuna damuwa akan yawaitar yaran da basu samu damar shiga makaranta ba, musamman a arewacin Najeriya, tare da daukar matakai na kyautata rayuwar su.
Wani bincike da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar tare da hadin guiwar hukumar kula da ilimin larabci da addinin Musulunci, da ma’aikatar mata ta jihar Sakkwato, sun tantance yara almajirai da ‘yan mata masu tasowa da adadin su ya kai 249,523 wadanda ke bukatar dauki.
A kan hakan ne asusun na UNICEF tare da samun tallafin kudi daga gidauniyar Eleva dake kasar Burtaniya, ta samar da wasu cibiyoyi domin koya wa wadannan yara dabarun samun rayuwa kyakkyawa a nan gaba.