Fadar White House ta Amurka tace Ukraine ta samu gagarumar nasara a cikin sa’a 72 a hare-haren da ta kai wa dakarun Rasha a tsakiyar yankin Zaporizhzhia.
A farkon makon nan, sojojin na Ukraine suka ce sun kama wani matsuguni a garin Robotyne, wanda hakan ya buɗe musu hanyar kai wa ga manyan birane na kudancin ƙasar, in ji Ministan wajen Ukraine.
Gwamnatin birnin Kyiv na fama kan yadda za ta iya kutsawa don shiga yankunan da dakarun Rasha suka ja daga, masu tsananin tsaro a Zaporizhzhia, yayin da a daya bangaren take ƙoƙarin ganin ta jure hare-haren da Rashar ke kai wa yankin gabashi.
Haka kuma wani babban jami’in Ukraine yace jiragen yakinsu sunyi barin wuta kan dakarun Rasha.
Wannan dai na zuwa dai-dai lokacin da ma’aikatar tsaron Rasha ke ikirarin tarwatsa jiragen yakin Ukraine 281 cikin mako guda, ciki harda 29 daga yammacin kasar. Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da dukkanin iƙirarin nasarar da kowanne ɓangare ke yi.