Toshon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido tare da Dan sa Kuma Santurakin Dutse Alhaji Mustapha Sule Lamido, sun yiwa Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ta’aziyar rasuwar Dan uwansa.
Wannan na kunshen cikin wata sanarwa da Mai taimakawa Gwamna Badaru kan Sabbin Kafafen Sadarwa Auwal Danladi Sankara, ya rabawa manema labarai ta shafinsa na Facebook.
Haka kuma ya ce Kwamishinoni da Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, da masu bawa Gwamna Shawara da yan Kasuwa da Shugabannin Gargajiya da sauran su na daga cikin wadanda suka yiwa Gwamna Ta’aziya.