A wani cigaban kuma, Tsohon Atoni-Janar na Tarayya, Cif Bola Ajibola, kuma Alkalin Kotun Duniya, ya rasu da sanyin safiyar yau lahdi.
Marigayin wanda ya kafa jami’ar Crescent, Abeokuta ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
Babban yaron marigayi masanin shari’a, Segun Ajibola, SAN, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta.
A yau ne ake sa ran za a yi jana’izar marigayin Cif Bola Ajibola a Abeokuta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.