Tsaro: Gwamnan Jihar Zamfara Ya Tafi Neman Mafita A Dubai

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle zai gana da masana akan tsaro a kasar Dubai, da ke hadadiyyar daular larabawa, don tattaunawa akan hanyoyin magance rashi tsaro a jihar.

Gwamnan wanda ya tafi kasar Saudiyya domin yin Umrah a jiya lahadi, 16 ga watan Yuni shekara 2019, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban darakta na al’amuran yada labarai na gidan gwamnati, Alhaji Yusuf Idris.

Alhaji Yusuf ya ce gwamnan zai wuce kasar ta Dubai bayan ya kammala Umrar sa, inda zai hadu da kwararrun masana akan tsaro don samun hanyoyi da suka fi dacewa wajen kawo karshen aikin ta’addanci a jihar.

Ya kara da cewa, gwamnan zai gana da hukumomi a kasar Saudiyya don a sako wani dan jihar mai suna Alaramma Ibrahim da kasar ke rike da shi, na tsawon shekaru biyu bisa zargin aikata laifin safarar kwaya, wanda aka gano cewa an saka masa ne a cikin kayan sa, a babban tashar jirgin sama na malam Aminu Kano da ke jihar Kano.

A karshe, Ya ce, gwamnan zai gana da ma’aikata daga bankin cigaban Afirka (African Development Bank) da masu zuba jari, akan batun saka jari a jihar Zamfara domin farfado da tattalin arzikin jihar.

InsurgencyZamfara
Comments (0)
Add Comment