Hukumar yan sanda ta kasa ta zata hada hannu da kwamatin kasa da kasa na hukumar agaji ta Red Cross da sauran hukumomin cigaba, wajen bayar da horo ga sabuwar rundunar SWAT da ta maye gurbin rundunar yan sanda ta musamman dake yaki da ayyukan fashi da makami wato SARS.

Kusan jami’ai 1,850 ne ake sa ran zasu halarci shirin bayar da horon na tsawon makonni 3, wanda za’a gudanar a makarantar baiwa yan sanda horo dake Ila Oragun a jihar Osun, da kuma ta Ende Hills dake jihar Nassarawa.
Kakakin hukumar Frank Mba, yace jami’an sabuwar rundunar ta SWAT, zasu karbi horo ne kan dokokin kiyaye dan adam da hakkokinsa, makamar jami’in dan sanda a halin rikici, kamawa da kuma tsare mai laifi da dai makamantansu.
- Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kara filayen noman shinkafa zuwa hekta 500,000 nan da shekarar 2030
- Gwamnomin Jam’iyyar PDP sunyi watsi da shirin yin kawance domin kawar jam’iyyar APC
- Ƴan Nijar mazauna Libya sun buƙaci gwamnatin Nijar ta kai musu ɗauki
- Za a kammala sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano cikin wata 14 – Ministan ayyuka
- Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti don nazarin tasirin sabon harajin Amurka
Masu gudanar da shirin bada horon sun hadar da jami’ai daga hukumomin cigaba, kwararru a fannin tsaro da kuma yan fafutuka daga kungiyoyn fararen hula.