Trump ya ƙaƙaba wa Najeriya sabon harajin kashi 14

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da haka ne a ranar Laraba, inda ya ce daga yanzu za a caji kashi 14 kan duk kayayyakin Najeriya da za su shiga ƙasar.

Sai dai mutane na ganin cewa watakila sabon harajin na Amurka ya shafi dangantakar ƙasashen biyu.

A cewar gwamnatin Trump, Najeriya ita ma ta saka wa kayayyakin Amurka da za su shiga ƙasar harajin kashi 27, inda ta ce abin bai yi wa kasuwancin Amurka kyau ba.

Ana ganin cewa mai yiwuwa hakan ne ya sa Amurkar ita ma ta saka harajin ramako ga Najeriya.

“Mun ƙaƙaba sabon harajin ga ƙasashen da ba sa yi mana daidai,” in ji Trump.

Kenya da Ghana da Ethiopia da Uganda da Senegal da kuma Laberiya na cikin ƙasashen da za su biya harajin da ya kai kashi 10.

Comments (0)
Add Comment