Tinubu ya tsawaita wa’adin shugabancin shugabar hukumar shigi da fici ta kasa, Kemi Nandap

Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsawaita wa’adin shugabancin shugabar hukumar shigi da fici ta kasaa, Kemi Nandap.

Nandap ta fara aiki ne a hukumar a ranar 9 ga Oktoban 1989.

Tinubu ya naɗa ta shugabar hukumar ne wato kwantura-janar a ranar 1 ga Maris na shekarar 2024, domin ta jagoranci hukumar zuwa ranar 31 ga Agustan 2025.

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce saboda nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Nadap ne ya sa shugaban ƙasar ya tsawaita shugabancinta zuwa 31 ga Disamban 2026.

Ya ce a ƙarƙashin jagorancinta an samu ci gaba da dama, musamman wajen zamanantar da ayyukan hukumar da tabbatar da kula da iyakokin ƙasar.

Comments (0)
Add Comment