Tinubu ya tsammaci sakayyar alheri daga ‘yan Jigawa a zaben 2027 – Gwamna Namadi

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce ya kamata Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsammaci sakayyar alheri daga ‘yan Jigawa a zaben 2027 mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin tallafin kudi na gwamnatin tarayya karo na biyu da aka gudanar a Dutse.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta bullo da tsare-tsare daban-daban na tallafawa mutane, don magance matsalar fatara da yunwa a fadin kasar nan, da suka hada da tallafin kudi na Cash Transfer, shirin N-Power, ciyar da Makarantu, da kuma shirin samar da tallafi na gwamnati (GEEP).

Gwamna Namadi ya bayyana cewa a karkashin kashi na biyu na tallafin kudi, kimanin marasa galihu dubu ashirin da uku ne za su amfana, inda za su samu naira dubu saba’in da biyar kowanne.

Comments (0)
Add Comment