Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa kudirin gyaran haraji da ke gaban Majalisar Dokoki ta Kasa ya zama doka mai amfani da tasiri.
Wannan kira ya zo ne bayan watanni hudu da aikewa da kudirin ga Majalisar don yin nazari da amincewa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wani zaman jin ra’ayi da Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa ya shirya a Abuja ranar Litinin, inda masu ruwa da tsaki daban-daban suka nuna goyon baya ga dokokin da aka gabatar.
Sanata Sani Musa, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalissar Dattawa, ya bayyana cewa Tinubu ya bukaci samar da doka mai amfani daga kudirin harajin da ya aika musu tun watan Oktoban bara.