Tinubu ya nada Dr Abdullahi Mustapha a matsayin darakta janar na hukumar makamashi ta kasa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Dr Abdullahi Mustapha a matsayin Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN).

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce shugaban kasar na sa ran sabon shugaban hukumar makamashin zai yi aiki mai kyau a yunkurin gwamnatinsa na habaka hanyoyin samar da makamashin don bunkasa masana’antu a kowane bangare na kasar nan. Dokta Mustapha ya yi aiki sama da shekaru goma a Hukumar Kula da Man Fetur ta kasa (NUPRC) tare da gogewa sosai a fannin makamashi da fasahar sararin samaniya.

Comments (0)
Add Comment