Shugaban kasa Bola Tinubu ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma al’ummar jihar Zamfara kan haɗarin kwale-kwale da ya rutsa da wasu manoma sama da 40 a a karamar hukumar Gummi, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.
Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban bai ji ɗadin lamarin da ya afku ba.
Shugaban kasar ya yi alkwarin bayar da tallafi ga waɗanda lamarin ya rutsa da ƴan uwansu.
Shugaba Tinubu ya bai wa hukumomin bayar da agaji da su gaggauta gudanar da bincike kan batun kifewar kwale-kwalen da kuma ambaliya da aka samu a yankin domin tallafawa mutane.
Ya kuma umarci hukumomin da su yi aiki tare da gwamnatin jihar Zamfara domin ganin yadda za a tallafawa mutanen da abin ya shafa.