Tinubu Ya Kalubalanci Karar Da Labour Party Da Peter Obi Suka Shigar Na Soke Zabensa

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kalubalanci cancantar karar da jam’iyyar Labour Party, da dan takararta, Peter Obi, suka shigar na soke zabensa.

Tinubu, a wata takaddama ta farko da ya shigar tare da zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya ci gaba da cewa, Obi ya rasa nasarar sa ne domin ya shigar da kara domin kalubalantar nasarar da ya samu a zaben.

Ya kara da cewa ba a tantance Obi da inganci ba don ya tsaya takarar shugaban kasa kamar yadda ya dace da tanadin doka na 77 (2) da (3) na dokar zabe, 2022.

Ya dage cewa ba a sami sunan Obi a rajistar mambobin jam’iyyar LP ba, inda ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ne daga jam’iyyar PDP, kasa da kwanaki 30 a gudanar da zaben fidda gwani da ya kawo shi a matsayin dan takarar shugaban kasa. Da yake gabatar da dalilan da suka sa ya lashe zaben shugaban kasa, Tinubu, a cikin karar farko da ya shigar ta hannun tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Cif Wole Olanipekun, SAN, ya ce daidaito da kuma tarihin sa na kwarewa a aikin gwamnati ne ya sa miliyoyin mutane su ka so shi.

Comments (0)
Add Comment