Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin Kamfanin NNPCL

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar na NNPCL, inda ya maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce hakan ya faru ne sakamakon wani garambawul da shugaban ya yi wa kamfanin.

Sanarwar ta ce shugaba Bola Tinubu ya rushe hukumar gudanarwar kamfanin ƙarƙashin shugabancin Cif Pius Akinyelure da kuma Mele Kyari wanda shi ne shugaban kamfanin.

“Shugaba Tinubu ya rushe dukkan mambobin hukumar da aka naɗa ƙarƙashin Pius Akinyelure da Mele Kyari a 2023.” In ji sanarwar.

Comments (0)
Add Comment