Tinubu ya amince da yin sabbin nade-nade guda hudu

Tinubu ya amince da yin sabbin nade-nade guda hudu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mambobi hudu a majalisar gudanarwar Hukumar Raya da Kula da Abubuwan da Aka Samar a kasa (NCDMB). 

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Alhamis, ta bayyana cewa an yi wannan nadin ne domin cike guraben da ke akwai da kuma kara karfin hukumar. 

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda aka nada sun hada da Mr. Olusegun Omosehin daga Hukumar Inshorar ta kasa (NAICOM) da Injiniya Wole Ogunsanya daga Kungiyar Fasahar Man Fetur (PETAN). Hakazalika, Shugaba Tinubu ya amince da nadin Sam Onyechi wanda ke wakiltar Taron Tattaunawa kan Abubuwan da Aka Samar a kasa (NCCF) da Barrister Owei Oyanbo daga Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur. 

Shugaban kasa ya bukaci sabbin mambobin da su yi amfani da kwarewarsu da jajircewarsu don bunkasa ci gaban abubuwan da aka samar a cikin masana’antar man fetur da iskar gas. Sanarwar ta kara da cewa an yi wadannan nade-nade ne sakamakon sauya tsoffin wakilan da suka bar majalisar gudanarwar hukumar.

Comments (0)
Add Comment