Shugaban kasa bola tinubu ya amince da kirkirar sabbin jami’o’I da suka hada da jamai’ar tarayya ta aikin gona da cigaban ilimi a jihar Osun da kuma jami’ar fasaha ta tarayya a jihar Ekiti.
Bayanin hakan na kunshe cxikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu a yammacin jiya alhamis.
A cewar sa, shugaba Tinubu jami’ion na musamman zasu taimaka wajen cike gibin ilimi da ake dashi da kuma tallafawa mutenen yankin da jami’ion suke wajen bincike, kirkira da kuma tallafawa tattalin arkin kasa baki daya.
Tinubu ya kuma ce jami’oin zasu kasance tamkar wasu cibiyoyin horaswa ne domin bunkasa aikin gona, kimiyya da fasaha da kuma bunkasa gwagwarmayar kasa a tsaren tattalin arziki a duniya.
A cewar hakumar kula da jami’io ta kasa NUC, kawo yanzu gwamnatin tarayya tana da jumillar jami’oi 63 mallakin ta, sai jami’oi 63 mallakin gwamnatocin jihohi da kuma wasu jami’oi 149 masu zaman kansu a kasa.
Ko a farkon watannan ma dai sai da shugaban kasar ya amince da kirkirar jami’ar fasaha da muhalli a jihar Rivers.