Ministan babban birnin Najeriya Abuja, Nyesom Wike, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da fara ɗiban fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa na birnin tsawon wata biyu.
Wike ya bayyana haka ne yayin taron bayyana ayyukan da ma’aikatu ke yi shekara ɗaya da kafa gwamnatin ta Tinubu.
A makon gobe ne dai ake sa ran ƙaddamar da jigilar fasinjoji ƙwaryar birnin tarayyar.
Shugaban ƙasa zai ƙaddamar da layin dogon ranar 27 ga watan Mayu, sannan a fara jigilar mutane kyauta tsawon wata biyu.
Sai dai hukumar kula da birnin Abuja ta ce yanzu an mayar da ranar ƙaddamarwar zuwa 29 ga wata.