Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan murna kan lashe kyautar “Sunhak Peace Founders Award” na shekarar 2025.
Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya Talata.
A cewar sanarwar, shuagabn kasar ya jinjinawa Jonathan saboda jajircewarsa wajen fafutukar zaman lafiya da dimokuradiyya, yana mai cewa wannan kokari na kishin kasa ne da ya sa aka masa kallon mutumin kirki a duniya.
Lashe wannan kyauta yana nuna irin gagarumar gudunmawar da Jonathan ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta dimokuradiyya a Afirka da duniya baki daya. Tinubu ya tuna yadda Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 da ya kayar da shi, sannan ya mika mulki cikin lumana ga jam’iyyar adawa, wanda hakan ya kara daraja tsarin dimokuradiyyar kasar.