Tinubu gaban kansa ya yi wajen cire tallafin mai – IMF

Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce shugaba Tinubu gaban kansa ya yi wajen cire tallafin mai amma asusun bai ba shi shawarar yin hakan ba.

Wannan dai na ɗauke a wata hira da darektar Asusun a nahiyar Afirka, Abebe Selassie ta yi da manema labarai a birnin Washington wadda kuma aka ɗora sahfin X na IMF ɗin.

“Shawarar cire tallafin mai daga cikin gida ne. Shugaba Tinubu ne ya yi. Ba mu da shirye-shirye a Najeriya. Damar da muke da ita ba ta wuce tattaunawa ba, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe kamar Japan da Burtaniya.” Kamar yadda ta ce.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai jim kaɗan bayan rantsar da shi tun ma kafin ya shiga ofis.

Masu lura da al’amura dai ba su ɗora laifin cire tallafin mai da Tinubu ya yi a kan IMF ba kasancewar ya yi hakan ne tun kafin ya shiga ofis.

Sai dai an fi alaƙanta cire tallafin wutar lantarki da Tinubu ya yi da asusun na IMF.

  • BBC Hausa
Comments (0)
Add Comment