TETFund sun kara tallafin fasahar sadarwa zuwa Naira Milyan 100 ga jami’o’i

Sakataren zartarwa, asusun kula da manyan makarantu TETFund Sonny Echono, ya ce sun kara tallafin fasahar sadarwa zuwa Naira Milyan 100 ga jami’o’i da kuma Naira Milyan 50 ga makarantun kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi.

Ya ce wannan kafin shekarar 2022 lokacin da tallafin ya kasance N15m na jami’o’i da kuma N7.5m na kwalejin fasaha dana ilimi.

Ya yi wannan jawabi ne a Abuja a wajen kaddamar da wani taron bita na kwanaki uku kan ‘Aiwatar da Tsarin Gudanar da Koyon a zamance.

Ya ce karuwar tallafin tallafin ga fasahar sadarwana daya daga cikin abubuwan da TETFUND ke baiwa muhimanci domin koyo da koyarwa.

Ya ce sama da dalibai miliyan biyu da ma’aikatan manyan cibiyoyi a kasar nan ba da dadewa ba za su samu damar yin amfani da ilimin kimiyya ta yanar gizo . Echono ya ce taron wanda ya samu halartar daraktocin ICT daga cibiyoyi 253 masu cin gajiyar asusun, an yi shi ne domin cike gibin fasahar dijital a jami’o’i, da kwalejoji.

Comments (0)
Add Comment