Tchiani ya gabatar da kasafin kuɗin Jamhuriyar Nijar na 2025

Shugaban gwamnatin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya gabatar da sabon kasafin kudin kasar na shekara ta 2025.

A lokacin gabatarwar, Janar Tchani ya ce kasafin ya kai jimillar kuɗi CFA biliyan 3,033.33, wanda hakan ke nuna cewa an samu ƙari da kimanin kashi 4.13% a kan kasafin kuɗin 2024 mai jimillar kuɗi CFA 2,913.06.

A ƙarƙashin sabon kasafin kuɗin gwamnati za ta ɓulla da sabbin haraje-haraje da kuma sake dawo da wani harajin da aka soke a baya.

Sai dai kasafin ya tanadi ɗauke wasu haraje-harajen, kamar na kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su.

Kasafin kudin na 2025 na zuwa ne bayan tasirin da yaƙin Ukarine da kuma annobar korona suka yi a ƙasashen duniya, lamarin da ya shafi ƙasar ta Nijar.

Haka nan wannan ne kasafin farko da ƙasar za ta yi aiki da shi bayan alaƙar da ta ƙulla da ƙasashen Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin haɗakar ƙasashen AES.

Juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar, wanda ya hamɓarar da gwamnatin shugaban Mohamed Bazoum ya janyo taɓarɓarewar alaƙa tsakaninta da manyan maƙwaftanta kamar Najeriya da Benin.

Kafin juyin mulkin, Benin na taka muhimmiyar rawa a ɓangaren fitar da albarkatun man fetur ɗin Nijar zuwa ƙasashen ƙetare.

Haka nan al’ummar ƙasar na gudanar da hulɗar cinikayya mai girma tsakaninsu da Najeriya.

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment