Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yace tattaunawa da barayi ‘yan bindiga ita ce hanya mafi dacewa wajen dorewar zaman lafiya a jihar, inda yace baya dana sanin kasancewar gwamnatinsa ta bi wannan hanyar.
Matawalle ya fadi haka daidai lokacin da ake ta tofa albarkacin bakuna akan ingancin hanyoyin da ake bi wajen magance matsalar tsaro da ta ki ci, ta ki cinyewa a Arewa maso Yamma.
- Rundunar ƴansanda Najeriya za ta hukuta ƴansandan da aka rabawa kuɗi a bidiyo
- Akwai yiwuwar jefa ƴan Najeriya cikin duhu matuƙar gwamnati bata biya bashin Naira Triliyan huɗu ba
- An raba Naira Triliyan 1.57 a tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hakumomi a Najeriya – FAAC
- Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kara filayen noman shinkafa zuwa hekta 500,000 nan da shekarar 2030
- Gwamnomin Jam’iyyar PDP sunyi watsi da shirin yin kawance domin kawar jam’iyyar APC
Yace duk da tarin sojojin da aka kawo da kuma luguden wutar da ake ta yiwa barayi babu kakkautawa, karkashin gwamnatinsa, kashe-kashen barayi yan bindiga na cigaba da karuwa a wani lamari mai firgitarwa.