Tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka a rubu’i na huɗun shekarar 2024

Wasu sabbin alkaluma sun bayyana cewa Tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka a rubu’i na huɗun shekarar 2024, wanda kuma shine haɓɓaka mafi sauri a cikin shekara uku, kamar yadda alƙaluma suka nuna a jiya Talata.

Arziƙin cikin gida na Najeriya ya haɓɓaka da kashi 3.84%, sama da kashi 3.46% da aka samu a rubu’i na uku na shekarar ta 2024.

A rubu’i na biyu na shekarar ta 2024 tattalin arziƙin ya haɓɓaka ne da kashi 3.19% yayin da rubu’i na farko kuma ya haɓɓaka da kashi 2.98%.

Hukumar ƙididdiga ta kasa NBS ta ce ɓangaren tafiyar da ayyuka na tattalin arziƙin shi ne kan gaba wajen haɓɓaka, da kashi 5.7% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.

A shekarar ta 2024 jimilla, tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka ne da kashi 3.40% idan aka kwatanta da kashi 2.74% a 2023.

Duk da haka, haɓɓakar ba ta cimma alƙawarin da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɗauka na haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kashi 6% ba a shekarar ta 2024.

Comments (0)
Add Comment