Taimakawa gwamnatin Najeriya kamar taimakawa kai ne – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yace gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na bukatar taimako sakamakon rashin ayyukan yin matasa da kuma tarin yaran da basa zuwa makaranta abinda ya haifar da matsalolin tsaron da suka adadi kasar wadanda suka zama wajibi su taimaka mata.

Sanarwar da Abubakar ya rabawa manema labarai sakamakon bayyana Najeriya a matsayin ‘Cibiyar rashin ayyukan yi ta duniya‘ yace taimakawa gwamnatin mai ci wajen shawo kan wadannan dimbin matsalolin kamar taimakawa kai ne.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace abin takaici shine yadda gwamnatin ke kallon shawarwarin da suke bayarwa a baya a matsayin suka, yayin da ya danganta karuwar aikata laifuffuka da rashin ayyukan yi da ake fama da shi a Najeriya.

Abubakar yace hankalin sa ya tashi da rahotan da kamfanin Bloomberg ya gabatar wanda ya sanya Najeriya a matsayin ta farko wajen yawan matasan da basu da ayyukan yi a duniya wadanda yawan su ya kai kashi 33. 

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace sun dade suna gargadi akan wannan yanayi shi da wasu masu kishin kasa amma ba’ayi la’akari da gargadin nasu ba. Abubakar yace Najeriya ta samu kan ta cikin wannan yanayi ne sakamakon kawar da kan da gwamnati tayi daga manufofin inganta rayuwar kasar da kasuwanci irin na gwamnatin Obasanjo abinda ya kaiga wasu masu zuba jari suna ficewa daga cikin ta. 

Tsohon dan takaran shugaban kasar a Jam’iyyar PDP yace rashin kudin da ake fama da shi ya taimaka wajen sanya hannun gwamnati wajen harkokin kasuwanci wadanda  ‘yan kasuwa aka sani da yi, cikin su harda rashin dabarar sanya Dala biliyan guda da rabi wajen sake gyara matatar man Fatakwal. 

Abubakar yace abinda ya dace wannan gwamnati ta fahimta shine matsalar tsaron da ya addabi Najeriya ya samu ne sakamakon rashin ayyukan yi na matasa, abinda ke basu damar mayar da hankalin su wajen aikata laifuffuka maimakon ayyukan da zasu gina kasa. 

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace ya zama dole Yan kasa da dattawan da ake da su da suyi magana a daidai sauran lokacin da ake da shi wajen ceto Najeriya, domin kuwa wannan gwamnatin bata da dabarun shawo kann matsalolin da suka addabi kasar dole sai sun taimaka mata. Abubakar yace taimakon nasu ba wai saboda gwamnati mai ci bane, sai dai saboda jama’ar Najeriya baki daya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bada shawarar fitar da hannun gwamnati a harkokin man kasar kamar yadda akayi da kamfanin iskar gas shekaru 20 da suka gabata wanda ya samar da ribar Dala biliyan 18 da miliyan 300 ga gwamnati.

Abubakar ya kuma bukaci bunkasa harkar samar da ilimi da zummar ganin an kawar da yara sama da miliyan 13 da basa zuwa makaranta ta hanyar taimakawa iyayen su da abin masarufi.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci shigar da matasa cikin ayyukan inganta rayuwar jama’a, yayin da yake tsokaci kann shirin gwamnati na samar musu ayyuka dubu 774,000 a fadin kasar da ya dace a fara a watan Janairu.

Comments (0)
Add Comment