Sojoji sun ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga

Rundunar Sojin Najeriya ta daya a jihar Kaduna, ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya ta sojojin Najeriya, Lt-Col. Musa Yahaya, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Kaduna.

Yahaya ya ce an ceto wadanda aka yi garkuwa da su ranar Litinin.

Musa Yahaya ya bayyana cewa, a yayin farmakin, sojoji sun yi taho-mu-gama da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane, inda suka yi artabu da su.

Ya ce sun tunkare su kai tsaye wanda ya tilasta musu yin watsi da wadanda suka yi garkuwa da su tare da kai musu dauki da raunuka daban-daban.

Ya ce babban kwamandan runduna ta 1 ta sojin kasar nan da kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Maj-Gen. Bamidele Alabi ya yabawa sojojin bisa jajircewa da kwarewa da suka nuna kafin aikin da kuma lokacin gudanar da aikin.

Comments (0)
Add Comment