Sojin ruwan ƙasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan na gudanar da atisayen kwanaki biyu, domin inganta aikinsu.
A wani mataki na tauna tsakuwa kan barazanar hare-haren makamai masu linzami na Koriya ta Arewa.
Manufar Tisayen shi ne faɗaɗa ikonsu da horon da zai ba su damar kare teku kan hare-haren makaman nukiliya na ƙarƙashin teku da Arewar ta fara yi a baya-bayan nan.
Za su samu horo kan yadda za su iya gano makamin nukiliya da zarar an sanya shi cikin teku.
Inda za a sanya wasu motocin teku na musamman a matsayin kan-da-garki.
Wannan dai shine karon farko da kasashen ke gudanar makamancin atisayen cikin shekaru 5, domin tauna tsakuwa kan barazanar gwajin wasu makamai da Korea ta arewa ta soma.