Dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansar Yamma da ke yaƙi da ƴan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa sun hallaka wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Rusu.
Jami’in hulɗa da jama’a na dakarun, Laftana Kanal Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da lamarin.
Ya ce rundunar ta ce ta samu nasarar murƙushe shi ne yayin wani samame da suka kai ta ƙasa da sama zuwa matattarar ƴan bindiga da ke ƙauyen Bamamu a ƙaramar hukumar Tsafe cikin jihar Zamfara, inda suka kashe ƙarin wasu mutanen da kuma ƙwato tarin makamai.