Sojin Najeriya na sane da matsalar rashin tsaro dake addabar Arewacin kasar

Babban hafsan sojin Najeriya laftanal Janar Taoreed Lagbaja yayi alkawarin samar da dukkan tsare-tsaren da suka zama wajibi domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Taoreed Lagbaja ya yi wannan alkawari ne yayin wata ziyara da gwaman jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya kai masa a jiya litinin.

Ya ce suna sane da matsalar rashin tsaro a jihar Sokoto dama wasu yankuna na jihohin arewa maso yamma.

Taoreed Lagbaja, ya jaddada kwarin gwiwar da yake da shi kan kwamandan rundunar Hadarin daji Manjo Janar Godwin Mutkut, za iyi dukkan abinda ya dace domin samun zaman lafiya a yankunan.

Gwamna Ahmed Aliyu ya kuma godewa sojoji Najeriya dangane da irin kokarin da suke na yaki da yan ta’adda a jihohin arewa maso yammacin kasar nan, ya tabbatar da cewa gwamnatin zata ci gaba da mara musu baya.

Comments (0)
Add Comment