Shugaban Yan Kungiyar Taliban ya bukaci kasashen Duniya su dauki matakan gaggawa domin tallafawa yan gudun hijirar Afghanistan, wanda suke cigaba da fuskantar matsaloli.
A yan kwanakin nan, hukumomin bada Agaji na Duniya sun ce Afghanistan na cikin halin Kakanakayi kan matsalolin rashin kayan Jinkai da za’a kai kasar.
Kaso 97 na yan kasar suna fama da Talauci a cewar Hukumar Samarda Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ne ya tirsasawa wasu yin kaura daga inda suke zuwa manyan birane.
Da yake zantawa da gidan Talabijin na Al-jazeera Ministan Lura da Yan Gudun Hijira na Kasar Mista Khalil-Ur-Rahman Haqqini, ya ce dubban yan kasar sun kauracewa muhallansu, sai dai ya ce lamura sun fara daidaita a Afghanistan wanda hakan ya bawa kowa damar komawa gida.
Mista Haqqini, ya ce za’a bawa mutanen da suka dawo tallafi ta yadda zasu sake gina gidajen su idan sun ruguje.