A yau ne ake sa ran shugaban kasa Muhammad Buhari zai kaddamar da masana’antar shinkafa ta Darma a Katsina, kamar yadda sanarwar da mahukuntan sabon kamfanin suka fitar a jiya.
Kamfanin mallakin hamshakin dan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal ne. Kamfanin wanda a shirya kaddamarwar, yana injunan da ke sarrafa kansu tare da ingantattun injunan aiki na zamani wadanda za su samar da ingantacciyyar shinkafa.
Kamfanin shinkafa na Darma yana da damar samar da ton 120 na Shinkafa a kowace rana daidai da tan dubu 250 a kowace shekara.
Kari bisa haka, masana’antar tana da wata tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 3.2 wacce ke amfani da yayin shinkafa tare da wata na’urar lantarki domin kare muhalli daga gurbacewa kuma tashar ita ce irinta ta farko a masana’antun shinkafa a Najeriya.
An kuma kiyasta cewa kamfanin zai samar da ayyuka sama da dubu 100 wanda zai taimaka wajen rage rashin aikin yi tare da bunkasa harkokin tattalin arziki.