Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi murnar lashe zaben kasar da aka gudanar na kwanan nan.
Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya litinin, inda yace lashe zaben da gudanar da shi na daya daga cikin burin al’ummar duniya na dorewar demikiradiyya.
Kazalika Buhari ya bukaci sabon shugaban kasar akan ya tabbatar da hadin kan al’umma domin cikawa yan kasar burin su.
Tare jan hankalin al’umma wajan kawar da dukwani banbancin siyasa dake tsakanin su, tare da goyawa gwamantin shugaba Ebrahim Raisi baya wajan yaki da cutar corona a fadin kasar.
Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan zata kara dankon alaka dake tsakaninta da kasar ta Iran.