Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci goyon bayan gwamnoni akan bangarorin cigaba da za a ba wa fifiko

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci goyon bayan gwamnonin jihohin kasar nan domin kawo sauyi ga tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban kasar ya ce an fara shirin kawo sauyin ga tattalin arzikin da cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin naira.

Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan kiran ne a wajen kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa jiya a Abuja.

Bola Ahmed Tinubu ya kuma lissafo bangarori guda takwas da gwamnato za tafi bawa muhimmanci da kulawa cikin gaggawa sannan ya yi kira da a samar da tsare-tsaren bai daya da za su karfafa tattalin arziki wanda zai dace da bukatun talakawa da marasa galihu. Shugaban kasar ya tabbatar wa gwamnonin jihohin cewa gwamnatinsa za ta magance matsalolin da ke kawo cikas ga rayuwar ‘yan Najeriya, tare da mai da hankali kan tsaro, da tattalin arziki, da ayyukan yi, da noma, da samar da ababen more rayuwa, da manufofin kudi da kuma tallafin man fetur.

Comments (0)
Add Comment