Shugaban karamar hakumar Hadejia Alhaji Ahmad Abba Ari ya bayyana damuwar sa ga masu aikin tsaftar muhalli a garin Hadejia bisa rashin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Shugaban karamar hakumar ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya rufe wani gidan wanka na Usman Iya dake cikin garin Hadejia.
Abba Ari yace rashin tsafta ne ya tilasta karamar hakuamr rufe gidan wankan domin kare lafiyar al’umma.
Sannan yace an rufe gidan wankan har sai baba ta gani, idan bai cika sharudan da aka gindaya mas aba.
Sharudan sun hada da fadada sokaway, da kwashe kazantar da shiga cikin magudanan ruwa.
Sannan yayi kira ga masu gidanjen wanka su tabbatar da tsafta domin kare lafiyar jama’a.