Shugaban hukumar EFCC yayi gargadin cewa babu wani wanda yafi karfin hukumar ta bincike shi

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC Ola Olukoyede, yayi gargadin cewa babu wani wanda yafi karfin hukumar ta bincike shi.

Ola Olukoyede, ya yi wannan gargadin ne a Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahwa da sauran laifukka ta ICPC, Musa Adamu Aliyu, akan batun dakatacciyar ministar Jinkai da yaki da fatara ta kasa Betta Eddu.

Wani kundin bayanai ya bayyana yadda Betta Edu ta umurci Babbar akanta janar ta kasa da ta biya kudin da suka kai kimanin Naira Miliyan 585 ga wani asusun wata mata mai suna Bridget Mojisola.

Biyo bayan kiraye-kirayen yan kasa ne Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Edu inda ya umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da tayi cikakken bincike akan badakalar kudaden. Shugaban hukumar EFCCn yace babu wata maboya ga masu cin hanci da rashawa a gwamnatin shugaba Tinubu.

Comments (0)
Add Comment