Karon farko a cikin ƙasa da mako guda, shugaban Burkina Faso kaften Ibrahim Traore ya jagoranci taron ministoci a yau Alhamis, a cikin wani yanayi mai cike da ayoyin tambayoyi.
Tun farko, fadar shugaban ƙasar ta fitar da sanar cewa shugaba Traore da kansa ne ya jagoranci taron ministocin na yau alhamis 20 ga watan Yuni.
Da sanyi safiya, Traore ya bayyana cikin murmushi kuma ga alama babu batun damuwa a Tattare da shi.
Hankulan ƴan Burkina Faso sun kwanta
Kafin bayyanarsa a wannan Alhamis, ƴan Burkina Faso sun shiga ɗimuwa sakamakon rashin jin ɗuriyar shugaban ƙasar tun bayan hare-haren da ƴan ta’adda suka ƙaddamar kan wasu barikokin soji a ranar 11 ga watan nan na Yuni.
An shiga rudani ne tun daga lokacin da aka kai wadannan hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwar sojoji masu tarin yawa, inda daga nan kuma aka rawaito cewa sojoji sun fusata tare da yin bore a cikin barikoki da dama.
Kodayake rundunar tsaron kasar ta fitar wata sanarwa da ke musanta cewa an samu barkewar bore a cikin barikokin sojin kasar, amma a ranar Larabar da ta gabata ya kamata a ga shugaba Traore ya fito domin jagorantar taron majalisar ministocin kasar, to sai dai ba a yi wannan taro ba saboda rashin fitowarsa.
Bayan samun hatsaniyar, wasu bayanai sun nuna cewa, gwamnatin Mali ta tura sojojinta da kuma na Wagner da adadinsu ya kama daga 80 zuwa 120 zuwa birnin Ouagadougou, watakila domin bai wa Traore kariya, yayin da wata majiyar ta tabbatar wa jaridar Le Monde cewa shugaban ya shiga ɓuya ne.