Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya za ta taimakawa jamhuriyar Burundi a hanyoyi daban-daban idan ta kama, inda yace zai yi hakan domin hadin kan Afrika da ‘yan’uwantaka.
Shugaban kasar ya sanar da haka yau a fadar shugaban kasa dake Abuja lokacin da ya karbi bakuncin jakada na musamman na shugaban kasa Evariste Ndayishimiye wanda yazo da wani sako.
Ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na Burundi, Audace Niyonzima, yace shugaban kasarsa ya aiko da sakon sabuwar shekara ga ‘yan Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kuma yiwa kasarnan fatan alkhairi a babban zaben da aka shirya gudanarwa a watannin Fabrairu da Maris na bana.
Dangane da bukatar neman tallafi a bangaren samar da makamashi, musamman man fetur, daga shugaban kasar Burundi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ya san wahalar da kasa ke sha idan tana fama da karancin makamashi.
Daganan ya sha alwashin cewa zai sanya kamfanin mai na kasa ya duba bukatar.