Shugaba Buhari Zai Bar Mulki Bayan Inganta Tsaro Da Tattalin Arziki Fiye Da Yadda Ya Same Su A 2015

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce shugaban ƙasar Muhamadu Buhari zai bar mulki a yayin da harkar tsaro da tattalin arzikin ƙasar suka inganta fiye da yadda ya same su a shekarar 2015, lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ranar Litinin, da daddare.
Ranar 29 ga watan Mayu ne dai shugaban ƙasar zai sauka daga mulki bayan kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
Masu suka na zargin cewa harkar tsaron ƙasar ta taɓarɓare a ƙarƙashin mulkinsa, sakamakon zarginsa da son kai wajen naɗe-naɗen muƙamai musamman na tsaro a maimakon duba cancanta, ko tsarin raba dai-dai na muƙaman gwamnatin tarraya.
Adesina ya kare wannan mataki da cewa ana yin naɗin muƙaman manyan hafsoshin tsaron ƙasar ne bisa cancanta, domin a cewarsa bai kamata a siyasantar da harkar tsaro ba wajen naɗin muƙamai.
Mista Adesina, ya ce ko ma mene ne mutane za su ce, Buhari zai bar mulkin Najeriya a daidai lokacin da ƙasar ta inganta fiye da yadda ya same ta a shekarar 2015.

Comments (0)
Add Comment