Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon shugaban Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano Farfesa Abdulhameed Isa Dutse.
Marigarayin ya yiwa gwamnatin jihar Jigawa aiki tsakanin watan Fabrairun 1992 zuwa Fabrairun 1994 a matsayin kwamishinan lafiya, daga baya kuma ya zama sakataren gwamnatin jiha a karkashin mulkin tsohon gwamna Ali Sa’adu Birninkudu.
Shugaban kasar ya bayyana rasuwar marigayi a matsayin babban rashi ga fannin kiwon lafiya.
- Za a kammala sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano cikin wata 14 – Ministan ayyuka
- Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti don nazarin tasirin sabon harajin Amurka
- Jam’iyyun adawa ba zasu iya haɗa kansu don tunkarar APC a zaɓen shekarar 2027 ba – Bukola Saraki
- Dakarun Operation Delta Safe sun rusa haramtattun matatun mai guda 22 a cikin makon da ya gabata
- “Jam’iyyun hamayya na son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba” – Ganduje
A sanarwar da Mallam Garba Shehu ya bayar a madadin shugaban kasa ta bayyana cewar rasuwar marigayi ta haifar da gibi ga yan Nigeria wajen cigaba da amfana da kwararrun likitocinta da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bautawa al’umma.
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Asibitin Aminu Kano da Gwamnatin Jihar Jigawa da kungiyar likitoci bisa rasuwar kwararren likitan tare da adduar Allah Ya jikansa kuma saka shi a gidan Aljanna.