Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gazawar da gwamnoni 10 suka yi a majalisar dattawa a zaben 2023 na nufin babu tabbacin hanyar da za a bi don samun mulki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu Sunusi a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ya ce zabukan 2023 sun tabbatar da karuwar dimokuradiyyar musamman yadda masu kada kuri’a a Najeriya suke yi wajen zaben shugabanni.
Bayan ya saurari mai martaba sarkin da ya lissafo wasu ayyuka da gwamnati ta yi wa jihar Jigawa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari, da kuma bukatar a kara wasu.
shugaban ya yi alkawarin yin iyakar kokarinsa ga jihar a sauran lokacin da ya rage, kuma zai yi wa shugaban kasa mai jiran gado Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bayani, a kan wadancan bukatu, inda ya cewa matsalar samar da ruwan sha a Dutse na da matukar damuwa.
Sarkin ya mika godiyarsa ga gwamnatin Muhammadu Buhari kan yadda jihar Jigawa ta yi fice a fannin noman shinkafa, da amincewa da hanyar layin dogo zuwa Dutse daga Kano da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar, daukacin al’ummar kasa da ma makwaftan da suka fuskanci rashin tsaro a baya. .
Ya kuma tunatar da irin rawar da Najeriya ta taka wajen ‘yantar da kasar Angola, ganin yadda kasar ta yi amfani da girmanta da albarkatunta wajen taimakawa ‘yan uwantaka na Afirka.