Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na kasar Saudiyya a wata ziyarar aiki ta kwanaki 8 zuwa gabas ta tsakiya.
Jirgin fadar shugaban kasa dauke shugaban kasa da wasu mukarraban sa ya Tashi a filin jiragen sama na Nmamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja da misalin karfe 9 da mintuna 10 na safe, ya kuma sauka a filin jirgin sama na Prince Muhammad Ibn Abdulaziz dake birnin Madina da yammacin yau misalin karfe 5 na yamma.
Yayin zaman sa a Madina shugaba Buhari zai gudanar da wajiban salloli 5 na yau da kullum, tare da sallahr Asham a masallacin manzon Allah SAW, kafin ya tafi Makka da yammacin gobe Laraba domin gudanar da Umara.
Kakakin shugaban kasa Mallam Garba Shehu a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya bayyana cewa ziyarar shugaban kasa ta yau 11 ga wata zuwa 19 wata zata kasance bulaguro na karshe zuwa Saudiyya a matsayin shugaban kasa.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, shugaba Buhari ya gudanar da Umara ta karshe a shakerar 2021.