Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da Daftarin Cigaban Kasa na shekarar 2021 zuwa 2025.
Majalisar Zartarwa ce ta amince da Daftarin ne tun cikin watan Nuwamba na wannan shekara, wanda aka kaddamar dashi a yau a fadar shugaban Kasa da ke Abuja.
Kafin gabatar da Daftarin a hukumance, Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa sabon Daftarin ya maye gurbin Daftarin Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na shekarar 2017 zuwa 2020.
Ministar ta ce Daftarin ya kushi hanyoyin da za’a bunkasa cigaban Kasa, a fannin Kimiyya da Fasaha, ta yadda hakan zai tafi da sauran kasashen Duniya.
Da yake gabatar da Daftarin, Shugaba Buhari ya samu dafawar Mataimakinsa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha Gida, da Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, da kuma Ministar Kudi, Kasafi da TsareTsare Zainab Ahmed.