Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron majalisar dinkin duniya karo na 76.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa dake birnin New York, ya bayar da labarin cewa Shugaba Buhari ya sauka a filin jiragen sama na Kennedy dake birnin New York da misalin karfe 4 na yamma agogon birnin.
Shugaban kasar ya samu tarbar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, da Wakilin Najeriya na dindindin a majalisar dinkin duniya, Tijjani Muhammad Bande, da sauransu.
Buhari zai kasance shugaban kasa na biyu da zai gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniyar a rana ta hudu da fara taron, da misalin karfe 9 na safe agogon can a ranar Juma’a mai zuwa, inda zai yi magana akan taken taron da sauran matsalolin dake fuskantar duniya.