Shawarwari 5 ga masu son fara koyon ilimin haɗa manhajin Kwamputa (programming)

Wato a halin yau da muke ciki rashin kyakkyawar kulawa da shawarwari ya hana matasa da dama fara wannan harkar ta computer gaba daya. Duk da tarin shawarwari da dabaru da kwararru suke bayarwa hakan bai hana mu samum nakasu a wurare da dama ba. A yau na kawo wasu shawarwari a takaice ga ma’abota son fara koyan programming kamar haka:

  1. Ka zabi bangare – akwai bangarori da suke a programming kamar yadda na lissafo su da kuma abubuwanda mutum yake bukata a wani rubutu na “Yaya AKe Zama Developer?”, kamar software development, web development da system development. Anan mutum ya kamata ya zabi wane bangare ne da yake so kafin ya fara.
  2. Ka saita lokacin koyo – ya kamata ka saita lokacin koyo misali da wane language ya kamata ka fara? Idan ka gama da shi wanne ya kamata ka shiga da sauransu. Rashin yin haka yana kai mutum ga fadawa wrong language kamar yadda muke kira, misali kanason gina website kawai sai ka fara koyon COBOL kawai dan shima programming language ne.
  3. Nemi kayan aiki – kafin ka fara programming ya kamata kasan da cewa kowane language yana da tsari da kuma kayan aiki da yake bukata. Misali idan zakayi python dole sai kayi installing python a system naka, tare da code editors. Haka idan zakayi C++ misali kana bukatar Dev-C++, Turbo da sauransu, ko kuma XAMPP a PHP/SQL da editors da sauran kayayyakin da zaka iya hukata, ya dai danganta da language din.
  4. Kayi tambaya – Abunda kake bukatar karin haske akai, ko gina wani algorithm ko kuma wani wuri da ya shige maka duhu, abu ne mai sauki ka tambayi kwararru. Akwai developers websites da dama da zaka iya yin tambaya kuma watakila ma abunda zaka tambaya wani ya riga ka, kaga sai dai kaga amsoshi kawai.
  5. Tsara project dinka – Ya kamata bayan ka fara koyon programming ka tsara wane abu kakeson ginawa – wato project naka. Hakan zai baka damar yin tunani mai zurfi da kuma samun ilimi mai yawa a lokacin da kake gina wannan abu. Zai baka damar kwarewa ko yin zurfi a wani bangare kamar language, algorithm da sauransu.

Wadannan shawarwari ne a takaice da zasu iya taimakawa idan ka san su kafin ka fara koyon programming. Sai dai a kullum abunda ake kara fadakar damu dashi juriya, hakuri da kuma jajircewa.

Mohiddeen Ahmad

ComputerProgramming
Comments (0)
Add Comment