A yunkurin gwamnatin jihara Jigawa na bude makarantu bayan samun sahalewa daga gwamnatin tarayya, shirye-shirye sun fara kankama don ganin an bude makarantu.
A wata sanarwa da mai bayar da shawara kan ilimi mai zurfi ga gwamnan jihar Jigawa Muhammad T Muhammad ya fitar,ta bayyana cewa bayan karbar rahoton kwamitin da gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kafa karkashin jagorancin kwamishin ilimin kimiyya da fasaha aka amince da cewa kafin bude makarantun a gwamnatin jiha zata yi abubuwa kamar haka;
1. A tabbatar da cewa an yi feshin maganin sauro a kowacce makaranta cikin gaggawa kafin komawa
2. Dukkan wasu kayayyaki na kariya dole ne a samar da su
3. Za a gyara duk dakunan duba marasa lafiya na makarantu
4. Duk manyan asibitocin kusa da makarantu zasu bayar da cikakkiyar kulawar gaggauwa ta musamman ga dalibai
- Kotu ta sa ranar yanke hukunci ga masu fasaƙaurin tururuwa
- Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamna Namadi ya nemi afuwarta kan yaga katin jam’iyyarta da yayi
- Tinubu ya yabawa Kungiyar ECOWAS bisa jajircewarta wajen karfafa hadin kai da cigaban yankin
- Matsalar wuta na ƙara ƙamari a jihohin Kano da makwabta
- Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 5 a Jihar Gombe
5. Za a kirkiro wakilan kula da lafiya a makarantu
6. Za a raba gidan sauro ga daliban makarantun kwana
7. Ma’aikatun gwamnati da sauran hukumomi zasu tattabatar an yi bi dokokin kariya daga COVID-19
8. Za a habaka shirye-shiryen wayar da kai don kariya
9. Al’umma da kungiyoyin cigaban gari da masu zaman kansu da kuma kwamitin cikin makaranta zasu iya bayar da tasu gudunmuwar wajen tabbatar da samun nasarar bude makarantu.

10. Ranar Litinin 12 ga Oktoba za a sake wani zaman domin tattaunawa tare da mahukunta kan shirin bude makarantun gaba da sakandire.
A cigaba da addu’a domin neman sauki wannan halin da ake ciki.