Sarkin Yaƙin Yarabawa, Gani Adams ya caccaki shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan halin tsadar rayuwa da ƙasar ke ciki.
Fitaccen mai fafutikar kare muradun Yarabawan ya buƙaci shugaban ya mayar da tallafin man fetur da ya cire tun bayan hawansa kan mulki.
Cikin wata wasika da ya rubuta wa shugaban mai taken “Shugaba Tinubu lokaci na tafiya’, Adams ya buƙaci Tinubu da ya janye wasu matakai masu tsauri da gwamnatinsa ta ɓullo da su.
Ya ce ya rubuta wasiƙar ce a matsayinsa na ɗaya daga cikin ƴan Najeriya sama da miliyan 200 domin bayyana masa halin da ƙasar ke ciki.
Mista Adams ya kuma zargi shugabannin Najeriya da suka gabata da jefa ƙasar cikin halin da take ciki.
“Maganar gaskiya ita ce, shugabanni da suka gabata, tun daga 1960, sun bai wa ƴan Najeriya kunya musamman ta hanyar shugabanci maras inganci da suka yi da kuma almubazzaranci da dukiyar ƙasa,” in ji Adams.
Ya ce lokacin da Tinubu ya fara yaƙin neman zaɓen 2023, ƴan Najeriya da dama sun amince cewa a matsayinsa na ɗan dimokraɗiyya, zai iya yin shugabanci nagari fiye da wanda ya gada Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa a zamaninsa ne talauci da rashin tsaro ya ƙaru daga 2015 zuwa 2023.
Sai dai sarkin yaƙin Yarabawan ya ce akasin haka suke gani yanzu tun bayan hawan Tinubu kan mulki.
“Al’amuran da suke faruwa a yanzu na nuna cewa fatan da mutane ke da shi game da kai ya dusashe”, in ji shi.
“Don haka maganar gaskiya shugaban ƙasa ka bai wa ‘yan Najeriya da dama kunya, waɗanda suka yi zaton cewa kai ne za ka fitar musu da kitse daga wuta”.
Ya kuma zargi shugaban ƙasar da ɓullo da matakan da suka tayar da farashin man fetur.
”A lokacin da ka zama shugaban Najeriya, farashin man fetur yana ƙasa da naira 200, amma a yanzu ya haura naira 1,000”, in ji mai fafutikar kare muradun Yarabawan.
”Haka ma a watan Mayun 2023, ana sayar da dala ƙasa da naira 740, amma a yanzu ta haura naira 1,600”, in ji shi.
Sarkin yaƙin Yarabawan ya kuma ce ya yi mamakin yadda shugaban wanda ke aiki da tsoffin na hannun damarsa lokacin da yake gwamnan Legas suka kasa fitar wa ƙasar da kitse daga wuta ta ɓangaren tattalin arziki.
“Manyan na hannun damanka a lokacin da kake gwamnan Legas, Wale Edun (ministan kuɗi) da Yemi Cardoso (Gwamnan CBN) su ne dai ke kula da tattalin arzikin ƙasar”.
“Waɗannan irin matakan tattalin arziki da tsare-tsare kuɗi suke ɗauka, kuma waɗanne irin bayanai suke yi maka a kullum da za su gamsar da kai cewa suna aikinsu yadda ya kamata?”
Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya janye ƙarin kuɗin man fetur da NNPCl ya yi a baya-bayan nan tare da janye duka matakan da ya ce sun janyo wa ƙasar faɗawa matsin tattalin arziki.
“Idan ba ka gaggauta janye waɗannan munanan matakan ba, to tabbas halin matsin da ake ciki a ƙasar nan zai ƙara munana”.